W.Yah 5:8 - Sabon Rai Don Kowa 20208 Bayan ya karɓa, sai halittu huɗun nan masu rai da kuma dattawan nan ashirin da huɗu suka fāɗi ƙasa a gaban Ɗan Ragon. Kowannensu yana da garaya kuma suna riƙe da kaskon zinariya cike da turare, waɗanda suke addu’o’in tsarkaka. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki8 Da ya ɗauki littafin, rayayyun halittan nan guda huɗu, da dattawan nan ashirin da huɗu, suka fāɗi gaban Ɗan Ragon, kowannensu yana riƙe da molo, da tasar zinariya a cike da turare, waɗanda suke addu'o'in tsarkaka. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Kowace a cikin halittu huɗu masu rai ɗin nan tana da fikafikai guda shida, tana kuma cike da idanu a ko’ina, har ma ƙarƙashin fikafikanta. Dare da rana ba sa fasa cewa, “ ‘Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki shi ne Ubangiji Allah Maɗaukaki,’ wanda yake a dā, wanda yake a yanzu, wanda kuma yake nan gaba.”