W.Yah 4:8 - Sabon Rai Don Kowa 20208 Kowace a cikin halittu huɗu masu rai ɗin nan tana da fikafikai guda shida, tana kuma cike da idanu a ko’ina, har ma ƙarƙashin fikafikanta. Dare da rana ba sa fasa cewa, “ ‘Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki shi ne Ubangiji Allah Maɗaukaki,’ wanda yake a dā, wanda yake a yanzu, wanda kuma yake nan gaba.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki8 Su rayayyun halittan nan huɗu kuwa, kowaccensu tana da fikafikai shida, jikinsu duk idanu ne ciki da waje, dare da rana kuwa ba sa daina waƙa, suna cewa, “Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki, Ubangiji Allah Maɗaukaki, Shi ne a dā, shi ne a yanzu, shi ne kuma a nan gaba!” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |