W.Yah 4:4 - Sabon Rai Don Kowa 20204 Kewaye da kursiyin kuwa akwai waɗansu kursiyoyi ashirin da huɗu, zaune a kansu kuwa dattawa ashirin da huɗu ne. Suna saye da fararen tufafi suna kuma da rawanin zinariya a kawunansu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki4 Kewaye da kursiyin kuwa akwai waɗansu kursiyai ashirin da huɗu, da dattawa ashirin da huɗu a zaune a kai, masu fararen tufafi, da kuma kambin zinariya a kansu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Na ga kursiyoyi inda waɗanda aka ba su ikon shari’a suke zama a kai. Sai na ga rayukan waɗanda aka yanke kawunansu saboda shaidarsu don Yesu saboda kuma maganar Allah. Ba su yi wa dabban nan ko siffarta sujada ba, ba su kuma sami alamarta a goshinsu ko a hannuwansu ba. Suka sāke rayuwa daga matattu, suka yi mulki tare da Kiristi shekaru dubu.