W.Yah 3:7 - Sabon Rai Don Kowa 20207 “Zuwa ga mala’ikan ikkilisiya a Filadelfiya, ka rubuta, Waɗannan su ne kalmomi, na wanda yake mai tsarki da kuma gaskiya, wanda yake riƙe da mabuɗin Dawuda. Abin da ya buɗe ba mai rufewa, abin da kuma ya rufe ba mai buɗewa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki7 “Ka kuma rubuta wa mala'ikan ikkilisiyar da take a Filadalfiya haka, ‘Ga maganar Mai Tsarkin nan, Mai gaskiya, wanda yake da mabuɗin Dawuda, wanda in ya buɗe, ba mai rufewa, in kuma ya rufe, ba mai buɗewa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ga abin da Ubangiji yana cewa, Mai Fansa da kuma Mai Tsarkin nan na Isra’ila gare shi wanda al’ummai suka rena suka kuma ki, ga bawan masu mulki. “Sarakuna za su gan ka su kuma miƙe tsaye, sarakuna za su gani su kuma rusuna, saboda Ubangiji, wanda yake mai aminci, Mai Tsarkin nan na Isra’ila, wanda ya zaɓe ka.”
Kowace a cikin halittu huɗu masu rai ɗin nan tana da fikafikai guda shida, tana kuma cike da idanu a ko’ina, har ma ƙarƙashin fikafikanta. Dare da rana ba sa fasa cewa, “ ‘Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki shi ne Ubangiji Allah Maɗaukaki,’ wanda yake a dā, wanda yake a yanzu, wanda kuma yake nan gaba.”