Sarakuna za su zama kamar iyayen reno, sarauniyoyinsu kuma za su yi renonku kamar uwaye. Za su rusuna a gabanki da fuskokinsu har ƙasa; za su lashe ƙura a ƙafafunki. Sa’an nan za ki san cewa ni ne Ubangiji; waɗanda suke sa zuciya gare ni ba za su sha kunya ba.”
Ƙofofinki kullum za su kasance a buɗe, ba za a ƙara rufe su da rana ko da dare ba, saboda mutane su kawo miki dukiyar al’ummai, sarakunansu za su kasance a gaba a jerin gwanon nasara.
Za ki sha madarar al’ummai a kuma shayar da ke da nonon sarauta. Sa’an nan za ki san cewa ni, Ubangiji, ni ne Mai Cetonki, Mai Fansarki, Mai Ikon nan na Yaƙub.