W.Yah 20:4 - Sabon Rai Don Kowa 20204 Na ga kursiyoyi inda waɗanda aka ba su ikon shari’a suke zama a kai. Sai na ga rayukan waɗanda aka yanke kawunansu saboda shaidarsu don Yesu saboda kuma maganar Allah. Ba su yi wa dabban nan ko siffarta sujada ba, ba su kuma sami alamarta a goshinsu ko a hannuwansu ba. Suka sāke rayuwa daga matattu, suka yi mulki tare da Kiristi shekaru dubu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki4 Sa'an nan na ga kursiyai, da waɗanda aka bai wa ikon hukunci, zaune a kai. Har wa yau, kuma na ga rayukan waɗanda aka fille wa kai saboda shaidar da suka yi wa Yesu, da kuma Maganar Allah, ba su kuwa yi wa dabbar nan da siffarta sujada ba, ba su kuma yarda a yi musu alamarta a goshinsu ko a hannunsu ba, sun sāke rayuwa, sun yi mulki tare da Almasihu har shekara dubu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Dabbar da ka gani, a dā ta taɓa kasancewa, a yanzu, ba ta, za tă kuma fito daga Abis zuwa ga hallakarta. Mazaunan duniya waɗanda ba a rubuta sunayensu a littafin rai tun kafin halittar duniya ba za su yi mamaki sa’ad da suka ga dabbar, domin a dā ta taɓa kasancewa, yanzu kuwa ba ta, duk da haka za tă dawo.