W.Yah 20:12 - Sabon Rai Don Kowa 202012 Sai na ga matattu, babba da yaro tsaye a gaban kursiyin, aka kuma buɗe littattafai. Aka buɗe wani littafi, wanda yake shi ne littafin rai. Aka yi wa matattu shari’a bisa ga abin da suka aikata yadda yake a rubuce a cikin littattafai. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki12 Sai na ga matattu manya da yara, a tsaitsaye a gaban kursiyin, aka kuma buɗe littattafai. Sai kuma aka buɗe wani littafi, wanda yake shi ne Littafin Rai. Aka kuwa yi wa matattu shari'a bisa ga abin da yake a rubuce a cikin littattafan, gwargwadon aikin da suka yi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Dabbar da ka gani, a dā ta taɓa kasancewa, a yanzu, ba ta, za tă kuma fito daga Abis zuwa ga hallakarta. Mazaunan duniya waɗanda ba a rubuta sunayensu a littafin rai tun kafin halittar duniya ba za su yi mamaki sa’ad da suka ga dabbar, domin a dā ta taɓa kasancewa, yanzu kuwa ba ta, duk da haka za tă dawo.