Muna kuwa da maganar annabawa da aka ƙara tabbatar mana, zai fi kyau in kuka lura da ita, kamar hasken da yake haskakawa a wuri mai duhu, har yă zuwa wayewar gari da kuma haskakawar tauraron asubahi a zukatanku.
Abokaina ƙaunatattu, yanzu, mu ’ya’yan Allah ne, kuma abin da za mu zama nan gaba ba a riga an bayyana ba. Sai dai mun san cewa sa’ad da Kiristi ya bayyana, za mu zama kamar sa, domin za mu gan shi kamar yadda yake.