Saboda haka, ka tuna fa, abin da ka karɓa ka kuma ji; ka yi biyayya da shi, ka kuma tuba. Amma in ba ka farka ba, zan zo kamar ɓarawo, ba kuwa za ka san lokacin da zan zo maka ba.
“Duba, yana zuwa cikin gizagizai, kowane ido kuwa zai gan shi, har da waɗanda suka soke shi”; dukan mutanen duniya kuwa “za su yi makoki dominsa.” Bari yă zama haka nan! Amin.
Amma ranar Ubangiji za tă zo kamar ɓarawo. Sammai za su ɓace da ruri, abubuwan da suke cikinsu za su ƙone, ƙasa kuma da dukan abin da yake cikinta za su tonu.
Saboda haka, kada ku shari’anta kome tun lokaci bai yi ba. Ku jira sai Ubangiji ya zo. Zai bayyana abin da yake a ɓoye a cikin duhu a sarari, zai kuma tone nufin zukatan mutane. A lokacin ne fa kowa zai karɓi yabo daga wurin Allah daidai gwargwado.
Ɗaya daga cikinsu mai suna Agabus, ya miƙe tsaye ya yi annabci ta wurin Ruhu cewa za a yi yunwa mai tsanani wadda za tă bazu a dukan duniyar Romawa (Wannan ya faru a zamanin mulkin Kalaudiyus.)