Ubangiji ba mai jinkiri ba ne wajen cika alkawarinsa, yadda waɗansunku suka fahimci jinkiri. Yana haƙuri da ku, ba ya so wani yă hallaka, sai dai kowa yă kai ga tuba.
Aka ƙone su da zafin wuta mai tsanani suka kuwa la’anci sunan Allah wanda yake da iko a kan waɗannan annoban, amma suka ƙi su tuba su kuma ɗaukaka shi.
Ku yi zaman sanin cewa haƙurin Ubangijinmu yana nufin ceto ne, kamar yadda ƙaunataccen ɗan’uwanmu Bulus ma ya rubuta muku da hikimar da Allah ya ba shi.
waɗanda dā ba su yi biyayya ba sa’ad da Allah ya jira da haƙuri a kwanaki Nuhu yayinda ake sassaƙa jirgi. A cikinsa mutane kima ne kawai, su takwas, aka kuɓutar ta ruwa,
Haka ma aikin Allah yake. Ya so yă nuna fushinsa yă kuma sanar da ikonsa, ya yi haka cikin haƙuri ƙwarai ga waɗanda suka cancanci fushinsa, waɗanda aka shirya domin hallaka?