Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




W.Yah 18:7 - Sabon Rai Don Kowa 2020

7 Ku ba ta isashen azaba da baƙin ciki kamar daraja da kuma jin daɗin da ta ba wa kanta. A zuciyarta takan yi taƙama, ta ce, ‘Ina zama kamar sarauniya; ni ba gwauruwa ba ce, kuma ba zan taɓa yin makoki ba.’

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

7 Yadda ta ɗaukaka kanta, ta yi almubazzaranci, Haka ku ma ku saka mata da azaba, da baƙin ciki gwargwadon haka. Tun da yake a birnin zuciyarta ta ce, ‘Ni sarauniya ce, a zaune nake, Ni ba gwauruwa ba ce, Ba ni da baƙin ciki kuma har abada!’

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




W.Yah 18:7
16 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Birnin da yake harka ke nan da take zaune lafiya. Ta ce wa kanta, “Ni ce, kuma babu kamata.” Dubi irin kangon da ta zama mana, mazaunin namun jeji! Duk wanda ya wuce ta sai ya yi mata tsaki yana kaɗa kai.


Yanzu birnin ya zama babu kowa a ciki, birnin da a dā yake cike da mutane! Yanzu birnin ya zama kamar gwauruwa, wadda a dā babba ce ita a cikin ƙasashe! Ita da take sarauniya a cikin larduna yanzu ta zama baiwa.


Ka faɗa wa sarki da kuma mahaifiyar sarauniya cewa, “Ku sauko daga kursiyinku, gama rawaninku na ɗaukaka za su fāɗi daga kawunanku.”


’Ya’yan sarki mata suna cikin matan da ake girmama; a hannun damarka kuwa ga amarya, sarauniya saye da ofir zinariya.


Yakan ce wa kansa, “Ba abin da zai girgiza ni; kullum zan yi murna ba zan taɓa shiga wahala ba.”


Fariyar zuciyarki ta yaudare ki, ke da kike zama can bisa duwatsu kika kuma yi gidanki a kan ƙwanƙoli, ke da kike ce wa kanki, ‘Wa zai iya saukar da ni ƙasa?’


Game da gwauraye masu ƙuruciya kuwa, kada ka sa su cikin wannan lissafi. Gama sa’ad da sha’awar jikinsu ta kāsa daurewa game da wa’adin da suka yi da Kiristi, sai su so yin aure.


Gama dukan al’ummai sun sha ruwan inabin haukan zinace zinacenta. Sarakunan duniya sun yi zina tare da ita, attajiran duniya kuma sun arzuta da almubazzarancinta.”


“Sa’ad da sarakunan duniya da suka yi zina da ita suka kuma yi tarayya cikin jin daɗinta suka ga hayaƙin ƙunarta, za su yi kuka da makoki saboda ita.


Sarki ya umarci Haman ya ce, “Tafi yanzu ka karɓi rigar da dokin, ka kuma yi yadda ka shawarta wa Mordekai, mutumin Yahudan nan, wanda yake zama a bakin ƙofar sarki. Kada ka kāsa yin kome daga cikin abin da ka faɗa.”


Za ki sha shi ki kuma lashe shi ƙaf; za ki buga shi da ƙasa ya yi rugu-rugu ki tsattsage nononki. Ni Ubangiji Mai Iko Duka na faɗa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ