Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




W.Yah 18:15 - Sabon Rai Don Kowa 2020

15 Attajiran da suka sayar da waɗannan kayayyaki suka kuma sami arzikinsu daga gare ta za su tsaya daga nesa, cike da tsoron ganin azabarta. Za su yi kuka da makoki

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

15 Attajiran waɗannan hajjoji da suka arzuta a game da ita, za su tsaya a can nesa don tsoron azabarta, suna kuka, suna baƙin ciki, suna cewa,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




W.Yah 18:15
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Gama dukan al’ummai sun sha ruwan inabin haukan zinace zinacenta. Sarakunan duniya sun yi zina tare da ita, attajiran duniya kuma sun arzuta da almubazzarancinta.”


Za su aske kawunansu saboda ke za su kuma sa tufafin makoki. Za su yi kuka dominki su yi ɓacin rai da kuma kuka mai zafi.


Da iyayengijin baranyar suka ga hanyar samun kuɗinsu ta toshe, sai suka kama Bulus da Sila suka ja su zuwa cikin kasuwa don su fuskanci hukuma.


Da yake koya musu, sai ya ce, “Ashe, ba a rubuce yake ba cewa, ‘Za a kira gidana, gidan addu’a na dukan al’ummai ba’? Amma ga shi kun mai da shi ‘kogon ’yan fashi.’”


Masu sayensu sun yanyanka su, suka kuwa tafi ba hukunci. Masu sayar da su sun ce, ‘Yabi Ubangiji, na yi arziki!’ Makiyayansu ma ba su ji tausayinsu ba.


kayayyakin zinariya, azurfa, duwatsu masu daraja da lu’ulu’ai; lallausan lilin, tufa masu ruwan shunayya, siliki da jan tufa; da kowane irin katakai masu ƙanshi da kayayyaki na kowane iri da aka yi da hauren giwa, katakai masu tsada, tagulla, baƙin ƙarfe da dutse mai sheƙi;


kayayyakin sinnamon da kayan yaji, na turaren wuta, mur da turare, na ruwan inabi da man zaitun, na gari mai laushi da alkama; shanu da tumaki; dawakai da kekunan doki, da jikuna da kuma rayukan mutane.


“Za su ce, ‘Amfanin da kike marmari ya kuɓuce. Dukan arzikinki da darajarki sun ɓace, ba kuwa za a ƙara samunsu ba.’


Za su zuba ƙura a kawunansu, da kuka da makoki za su yi ta kururuwa, “ ‘Kaito! Kaito, ya birni mai girma, inda dukan waɗanda suke da jiragen ruwa a teku suka arzuta da ɗumbun dukiyarsa! Cikin sa’a ɗaya ta hallaka!’


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ