W.Yah 13:10 - Sabon Rai Don Kowa 202010 Duk wanda aka ƙaddara ga bauta, ga bauta zai tafi. Duk wanda aka ƙaddara za a kashe da takobi, da takobin za a kashe shi. Wannan yana bukata haƙuri da aminci a gefen tsarkaka. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki10 Kowa aka ƙaddara wa bauta, sai ya je aikin bautar. Kowa kuwa ya yi kisa da takobi, to, kuwa da takobi za a kashe shi lalle. Wannan yana nuna jimiri da bangaskiya na tsarkaka. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Dabbar da ka gani, a dā ta taɓa kasancewa, a yanzu, ba ta, za tă kuma fito daga Abis zuwa ga hallakarta. Mazaunan duniya waɗanda ba a rubuta sunayensu a littafin rai tun kafin halittar duniya ba za su yi mamaki sa’ad da suka ga dabbar, domin a dā ta taɓa kasancewa, yanzu kuwa ba ta, duk da haka za tă dawo.