W.Yah 12:17 - Sabon Rai Don Kowa 202017 Sai macijin ya yi fushi da macen ya kuma koma wajen sauran zuriyarta don yă yaƙe su waɗannan waɗanda suke biyayya da umarnan Allah suke kuma riƙe da shaidar Yesu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki17 Macijin kuwa ya yi fushi da matar, ya tafi ya ɗaura yaƙi da sauran zuriyarta, wato, waɗanda suke kiyaye umarnin Allah, suke kuma shaidar Yesu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Na ga kursiyoyi inda waɗanda aka ba su ikon shari’a suke zama a kai. Sai na ga rayukan waɗanda aka yanke kawunansu saboda shaidarsu don Yesu saboda kuma maganar Allah. Ba su yi wa dabban nan ko siffarta sujada ba, ba su kuma sami alamarta a goshinsu ko a hannuwansu ba. Suka sāke rayuwa daga matattu, suka yi mulki tare da Kiristi shekaru dubu.