W.Yah 11:3 - Sabon Rai Don Kowa 20203 Zan kuma ba wa shaiduna nan biyu iko, za su kuwa yi annabci na kwanaki 1,260, saye da gwadon makoki.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki3 Zan kuma bai wa mashaidana biyu iko su yi annabci kwana dubu da metan da sittin, suna a saye da tsummoki.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Mutumin da yake sanye da tufafin lilin, wanda yake a saman ruwan kogin, ya ɗaga hannun damansa da kuma na hagunsa sama, sai na ji yana rantsuwa da wannan da yake raye har abada, yana cewa, “Zai kasance na ɗan lokaci, lokuta da rabin lokaci. Za a kammala waɗannan abubuwa, sa’ad da aka gama ragargaje ikon tsarkakan mutane.”
Na ga kursiyoyi inda waɗanda aka ba su ikon shari’a suke zama a kai. Sai na ga rayukan waɗanda aka yanke kawunansu saboda shaidarsu don Yesu saboda kuma maganar Allah. Ba su yi wa dabban nan ko siffarta sujada ba, ba su kuma sami alamarta a goshinsu ko a hannuwansu ba. Suka sāke rayuwa daga matattu, suka yi mulki tare da Kiristi shekaru dubu.