Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Waƙar Waƙoƙi 7:9 - Sabon Rai Don Kowa 2020

9 kuma bakinki ya yi kamar ruwan inabi mafi kyau. Bari ruwan inabi yă wuce kai tsaye zuwa ga ƙaunataccena, yana gudu a hankali a leɓuna da kuma haƙora.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

9 Bakinki kamar ruwan inabi mafi kyau ne. Idan haka ne bari ya bulbulo sosai zuwa ga ƙaunataccena, Ya gangara leɓunan masu barci.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Waƙar Waƙoƙi 7:9
18 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Bakinsa zaƙi ne kansa; komensa yana da kyau. Haka ƙaunataccena, abokina, yake ’yan matan Urushalima.


Sai na ji murya daga sama ta ce, “Rubuta, Masu albarka ne matattun da suka mutu cikin Ubangiji daga yanzu zuwa gaba.” “I, za su huta daga faman aikinsu, gama ayyukansu za su bi su,” in ji Ruhu.


Saboda haka, ta wurin Yesu, bari mu ci gaba da miƙa hadaya ta yabo ga Allah, yabon leɓuna da yake shaidar sunansa.


Bari maganarku kullum ta zama da ladabi da kuma daɗin ji, domin ku san amsar da ta dace ku ba wa kowa.


Kada wata ƙazamar magana ta fita daga bakunanku, sai dai abin da yake da amfani don gina waɗansu bisa ga bukatunsu. Ta haka maganarku za tă zama da amfani ga masu jinta.


Ku yi wannan domin kun san irin zamanin da kuke ciki. Lokaci ya yi da za ku farka daga barcinku, don cetonmu ya yi kusa yanzu fiye da lokacin da muka fara ba da gaskiya.


Na yi barci amma zuciyata tana a farke. Ku saurara! Ƙaunataccena yana ƙwanƙwasa ƙofa. “Buɗe mini, ’yar’uwata, ƙaunatacciyata, kurciyata, marar laifina. Kaina ya jiƙe da raɓa, gashina ya yi danshin ɗiɗɗigar dare.”


Kurciyata a kogon dutse, a wuraren ɓuya a gefen dutse, nuna mini fuskarki, bari in ji muryarki; gama muryarki da daɗi take, fuskarki kuma kyakkyawa ce.


Kalmomi masu daɗi suna kama da kakin zuma, mai zaƙi ga rai da kuma warkarwa ga ƙasusuwa.


Kada ka ƙyifce ido a ruwan inabi sa’ad da ya yi ja, sa’ad da yana da kyan gani a cikin ƙwarya, sa’ad da yana gangarawa sumul a maƙogwaro!


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ