Ka ɗauke ni mu gudu, mu yi sauri! Bari sarki yă kai ni gidansa. Muna farin ciki muna kuma murna tare da kai, za mu yabi ƙaunarka fiye da ruwan inabi. Daidai ne su girmama ka!
Na zo lambuna, ’yar’uwata, amaryata; na tattara mur nawa da kayan yajina. Na sha zumana da kuma kakinsa na sha ruwan inabina da kuma madarana. Ku ci, ku kuma sha, ya ku ƙawaye; ku sha ku ƙoshi, ya ƙaunatattu.
Sarki ya tashi cikin fushi, ya bar ruwan inabinsa, ya fita zuwa cikin lambun fada. Amma da Haman ya gane cewa sarki ya riga ya yanke shawara a kan ƙaddararsa, ya dakata domin yă roƙi sarauniya Esta saboda ransa.