Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Waƙar Waƙoƙi 1:4 - Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Ka ɗauke ni mu gudu, mu yi sauri! Bari sarki yă kai ni gidansa. Muna farin ciki muna kuma murna tare da kai, za mu yabi ƙaunarka fiye da ruwan inabi. Daidai ne su girmama ka!

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

4 Ka ɗauke ni mana, mu gudu, Ka zama sarkina, ka kai ni ɗakinka. Da yake kana nan za mu yi farin ciki, Za mu sha ruwan inabi, mu yi murna da ƙaunarki. Ya dace a ƙaunace ka!

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Waƙar Waƙoƙi 1:4
37 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ya sa a tuna da abubuwa masu banmamaki nasa; Ubangiji mai alheri ne mai tausayi kuma.


Ina gudu a kan hanyar umarnanka, gama ka ’yantar da zuciyata.


Zan gaggauta ba zan ɓata lokaci ba in yi biyayya da umarnanka.


Bari Isra’ila su yi farin ciki da Mahaliccinsu; bari mutanen Sihiyona su yi murna da Sarkinsu.


Waɗannan abubuwa ne nakan tuna sa’ad da nake faɗin abin da yake a raina, yadda dā nakan tafi tare da taron jama’a, ina bishe su a jere zuwa gidan Allah, da sowa ta farin ciki da kuma godiya a cikin taron biki.


Cikin haikalinka, ya Allah, mun yi tunani a kan ƙaunarka marar ƙarewa.


Raina zai ƙoshi kamar da abinci mafi kyau; da leɓunan rerawa bakina zai yabe ka.


Rabuwata da su ke nan sai na sami wanda zuciyata take ƙauna. Na riƙe shi, ban yarda yă tafi ba sai da na kawo shi gidan mahaifiyata, zuwa ɗakin wadda ta yi cikina.


Ƙaunarki abar farin ciki ne, ’yar’uwata, amaryata! Ƙaunarki ta fi ruwan inabi gamsuwa, ƙanshin turarenki kuma ya fi duk wani kayan yaji!


zai haɗiye mutuwa har abada. Ubangiji Mai Iko Duka zai share hawaye daga dukan fuskoki; zai kawar da kunyar mutanensa daga dukan duniya. Ubangiji ne ya faɗa.


Amma a cikin Ubangiji dukan zuriyar Isra’ila za su sami adalci za su kuwa yi yabo.


in tanada wa waɗanda suke baƙin ciki a Sihiyona, in maido musu rawani mai kyau a maimako na toka, man murna a maimako na makoki, da kuma rigar yabo a maimako na ruhun fid da zuciya. Za a ce da su itatuwan oak na adalci, shukin Ubangiji don bayyana darajarsa.


Zan ba da labarin alherin Ubangiji, ayyukan da suka sa a yabe shi, bisa ga dukan abubuwan da Ubangiji ya yi mana, I, ayyuka masu kyan da ya yi domin gidan Isra’ila, bisa ga jinƙansa da yawan alheransa.


Ubangiji ya bayyana mana a dā, yana cewa, “Na ƙaunace ku da madawwamiyar ƙauna; na janye ku da ƙauna marar iyaka.


Na bishe su da linzamin alheri da tausayi, da ragamar ƙauna; Na cire karkiya daga wuyansu na kuma rusuna na ciyar da su.


Ki rera, ya Diyar Sihiyona; ki tā da murya, ya Isra’ila! Ki yi murna ki kuma yi farin ciki da dukan zuciyarki, Ya Diyar Urushalima!


Ki yi murna ƙwarai, ya Diyar Urushalima! Ki yi sowa, Diyar Urushalima! Duba, ga sarkinki yana zuwa wurinki, mai adalci yana kuma da ceto, mai tawali’u yana kuma hawan jaki, yana a kan ɗan aholaki, a kan ’yar jaka.


“Amma yayinda suke kan tafiya garin sayen mai, sai ango ya iso. Budurwai da suke a shirye, suka shiga wajen bikin auren tare da shi. Aka kuma kulle ƙofa.


Amma mala’ikan ya ce musu, “Kada ku ji tsoro. Na kawo muku labari mai daɗi na farin ciki mai yawa ne wanda zai zama domin dukan mutane.


Sai ya ɗauki burodi ya yi godiya, ya kakkarya ya ba su, da cewa, “Wannan jikina ne, da aka bayar dominku. Ku riƙa yin haka don tunawa da ni.”


Amma ni, sa’ad da aka ɗaga ni daga ƙasa, zan ja dukan mutane gare ni.”


Ba mai iya zuwa wurina, sai dai in Uban da ya aiko ni ya jawo shi, ni kuwa zan tashe shi a rana ta ƙarshe.


Allah ya tashe mu tare da Kiristi, ya kuma ba mu wurin zama tare da shi a cikin mulkin samaniya.


Alheri yă tabbata ga dukan masu ƙaunar Ubangiji Yesu Kiristi da ƙauna marar ƙarewa.


Gama mu ne masu kaciya, mu da muke yi sujada ta wurin Ruhun Allah, mu da muke taƙama a cikin Kiristi Yesu, mu da ba mu dogara da ayyukan da ake gani ba,


Ku yi farin ciki a cikin Ubangiji kullum. Ina sāke gaya muku ku yi farin ciki!


Saboda haka, da yake muna kewaye da irin wannan taron shaidu mai girma, sai mu yar da duk abin da yake hana mu da kuma zunubin da yake saurin daure mu, mu kuma yi tseren da aka sa a gabanmu da nacewa.


Ko da yake ba ku taɓa ganinsa ba, kuna ƙaunarsa; kuma ko da yake ba kwa ganinsa yanzu, kun gaskata shi, kun kuma cika da farin ciki ƙwarai, wanda ya fi gaban faɗi,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ