Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Waƙar Waƙoƙi 1:16 - Sabon Rai Don Kowa 2020

16 Kai kyakkyawa ne, ƙaunataccena! Kai, kana ɗaukan hankali! Gadonmu koriyar ciyawa ce.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

16 Kai kyakkyawa ne ƙwarai, ya ƙaunataccena, kana da bansha'awa. Koriyar ciyawa ita ce gadonmu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Waƙar Waƙoƙi 1:16
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Kamar itacen gawasa a cikin itatuwan jeji haka ƙaunataccena yake a cikin samari. Ina farin ciki in zauna a inuwarsa, ’ya’yan itacensa suna da daɗin ɗanɗanon da nake so


Kai ne mafi kyau cikin mutane an kuma shafe leɓunanka da alheri, da yake Allah ya albarkace ka har abada.


Za su yi kyan gani da kuma bansha’awa! Hatsi zai sa samari su yi murna, sabon ruwan inabi kuma zai sa ’yan mata su yi farin ciki.


Duba! Abin ɗaukar Solomon ne, jarumawa sittin suke rakiya, zaɓaɓɓun sojojin Isra’ila,


Rundunarka za su so yin yaƙi a ranarka ta yaƙi. Saye cikin ɗaukaka mai tsarki, daga cikin ciki na safiya za ka karɓi raɓar ƙuruciyarka.


Ke kyakkyawa ce, ƙaunatacciyata! Kai, ke kyakkyawa ce! Idanunki kamar na kurciya ne.


Ƙaunataccena yana kama da barewa ko sagarin ƙishimi Duba! Ga shi can tsaye a bayan katangarmu, yana leƙe ta tagogi, yana kallo ta cikin asabari.


Na yi barci amma zuciyata tana a farke. Ku saurara! Ƙaunataccena yana ƙwanƙwasa ƙofa. “Buɗe mini, ’yar’uwata, ƙaunatacciyata, kurciyata, marar laifina. Kaina ya jiƙe da raɓa, gashina ya yi danshin ɗiɗɗigar dare.”


Na tashi don in buɗe wa ƙaunataccena, sai hannuna ya jiƙe sharkaf da mur, yatsotsina suna ɗiga da mur, a hannuwan ƙofar.


Kai! Ke kyakkyawa ce kuma kina sa ni jin daɗi, Ya ƙaunatacciya, da farin cikin da kike kawo!


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ