“Daga baya kuma, zan zuba Ruhuna a bisan dukan mutane. ’Ya’yanku maza da mata za su yi annabci, tsofaffinku za su yi mafarkai, matasanku za su ga wahayoyi.
Amma gaskiya nake gaya muku. Don amfaninku ne zan tafi. Sai ko na tafi, in ba haka ba Mai Taimakon nan ba zai zo muku ba. Amma in na tafi, zan aiko shi gare ku.
Ko da yake ni ba kome ba ne a cikin dukan mutanen Ubangiji, aka ba ni wannan baiwa mai daraja don in faɗa wa Al’ummai cewa saboda Kiristi akwai albarkun da suka wuce gaban misali.
Ka umarci waɗanda suke da arziki a wannan duniya kada su ɗaga kai ko su sa begensu a kan dukiyar da ba ta da tabbaci, sai dai su sa begensu ga Allah, wanda yake ba mu kome a yalwace don jin daɗinmu.