Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Rut 4:4 - Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Na ga ya kamata in jawo hankalinka ga batun in kuma ba da shawara ka saye shi a gaban waɗannan da suke zazzaune a nan da kuma a gaban dattawan jama’a. In kana so ka fanshe shi, to, sai ka yi. Amma in ba za ka yi ba, sai ka faɗa mini, don in sani. Gama babu wani mai izinin yin haka sai kai, ni ne kuwa na biye.” Sai ya ce, “Zan fansa.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

4 Don haka na ga ya kamata in sanar da kai cewa, ka saye ta a gaban waɗanda suke zaune a nan, da a gaban dattawan jama'a. Idan za ka fanshi gonar sai ka fanshe ta, idan kuwa ba za ka fansa ba, ka faɗa mini don in sani, gama daga kai sai ni muke da izinin fansar gonar.” Sai mutumin ya ce, “Zan fanshe ta.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Rut 4:4
12 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

A ƙarshe, ’yan’uwa, duk abin da yake na gaskiya, duk abin da yake na girmamawa, duk abin da yake daidai, duk abin da yake da tsarki, duk abin da yake kyakkyawa, duk abin da yake na sha’awa, in ma wani abu mafifici ne, ko ya cancanci yabo, ku yi tunani a kan irin abubuwan nan.


Gama muna iya ƙoƙari mu yi abin da yake daidai, ba a gaban Ubangiji kaɗai ba, amma a gaban mutane ma.


Idan kowa ya yi muku mugunta, kada ku sāka masa da mugunta. Ku lura don ku aikata abin da kowa zai iya gani cewa daidai ne.


Ko da yake za a ba da birnin ga Babiloniyawa, kai, ya Ubangiji Mai Iko Duka, ka ce mini, ‘Saye fili da azurfa ka kuma sa a shaida cinikin.’ ”


ba wa Ibrahim a matsayin mallakarsa a gaban dukan Hittiyawa waɗanda suka zo ƙofar birnin.


Ya ce, “A’a, ranka yă daɗe, ka ji ni, na ba ka filin, na kuma ba ka kogon da yake cikinsa. Na ba ka shi a gaban mutanena. Ka binne mataccenka.”


Sai dattawan garinsa su kira shi, su kuma yi masa magana. In ya nace yana cewa, “Ba na so in aure ta,”


Sai Na’omi ta ce wa surukarta, “Ubangiji yă yi masa albarka! Bai daina nuna alheri ga masu rai da matattu ba.” Ta ƙara da cewa, “Wannan mutum danginmu ne na kusa; shi ɗaya daga cikin danginmu mai fansa.”


Sai ya yi tambaya ya ce, “Ke wace ce?” Ta amsa ta ce, “Ni ce baranyarka Rut, ka rufe ni ta mayafinka da yake kai dangi, mai fansa ne na kusa.”


Ko da yake gaskiya ne ni dangi ne na kusa, amma akwai dangi mai fansa mafi kusa fiye da ni.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ