Rut 2:20 - Sabon Rai Don Kowa 202020 Sai Na’omi ta ce wa surukarta, “Ubangiji yă yi masa albarka! Bai daina nuna alheri ga masu rai da matattu ba.” Ta ƙara da cewa, “Wannan mutum danginmu ne na kusa; shi ɗaya daga cikin danginmu mai fansa.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki20 Na'omi ta ce wa Rut, “Ubangiji wanda bai daina nuna alheri ga masu rai da marigayan ba, ya sa masa albarka.” Ta ƙara da cewa, “Ai, mutumin, shi danginmu ne na kusa.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Na ga ya kamata in jawo hankalinka ga batun in kuma ba da shawara ka saye shi a gaban waɗannan da suke zazzaune a nan da kuma a gaban dattawan jama’a. In kana so ka fanshe shi, to, sai ka yi. Amma in ba za ka yi ba, sai ka faɗa mini, don in sani. Gama babu wani mai izinin yin haka sai kai, ni ne kuwa na biye.” Sai ya ce, “Zan fansa.”