Dubi irin ƙaunar da Uba ya ƙaunace mu da ita mana, har ana ce da mu ’ya’yan Allah! Haka kuwa muke! Dalilin da ya sa duniya ba tă san mu ba shi ne, don ba tă san shi ba.
Waɗanda suke rayuwa bisa ga mutuntaka sun kafa hankulansu a kan sha’awace-shawa’acen jiki; amma waɗanda suke rayuwa bisa ga Ruhu sun kafa hankulansu a kan abubuwan da Ruhu yake so.
Ku kam, ana mulkinku ba ta wurin mutuntaka ba, sai dai ta wurin Ruhu, in Ruhun Allah yana zaune a cikinku. In kuma wani ba shi da Ruhun Kiristi, shi ba na Kiristi ba ne.
“Duk da haka Isra’ilawa za su zama kamar yashi a bakin teku, da ba za a iya aunawa ko a ƙirga ba. A inda aka ce musu, ‘Ku ba mutanena ba ne,’ za a kira su ‘’ya’yan Allah mai rai.’
Waɗanda suke biyayya da umarnansa kuwa suna rayuwa a cikinsa, shi kuma a cikinsu. Ta haka muka san cewa yana raye a cikinmu. Mun san haka ta wurin Ruhun da ya ba mu.