Amma a yanzu da aka ’yantar da ku daga zunubi kuka kuma zama bayi ga Allah, ribar da kuka samu tana kai ga zaman tsarki, ƙarshenta kuwa rai madawwami ne.
ba makamin da aka ƙera don yă cuce ki da zai yi nasara, za ki kuma mayar da magana ga duk wanda ya zarge ki. Wannan ne gādon bayin Ubangiji, kuma wannan ita ce nasararsu daga gare ni,” in ji Ubangiji.
“Ruhun Ubangiji yana kaina, domin ya shafe ni, in yi wa matalauta wa’azin bishara. Ya aiko ni in yi shelar ’yanci ga ’yan kurkuku, in kuma buɗe idanun makafi, in ba da ’yanci ga waɗanda aka danne.