Ku ’yan’uwana, an kira ku ga zama ’yantattu. Amma kada ku yi amfani da ’yancinku don aikata ayyukan mutuntaka a maimakon haka, ku yi hidimar juna da ƙauna.
Na faɗa haka ne domin waɗansu mutanen da aka rubuta hukuncinsu tun dā sun shiga cikinku a ɓoye. Su fa marasa tsoron Allah ne. Su ne waɗanda suka mai da alherin Allahnmu ya zama dalilin yin fasikanci, suna kuma mūsun Yesu Kiristi wanda shi ne Makaɗaici Mai Iko Duka da kuma Ubangijinmu.