Gama Ubangiji Allahnku ne Allahn alloli da Ubangijin iyayengiji, Allah mai girma, mai ƙarfi da kuma mai banrazana, wanda ba ya sonkai, ba ya cin hanci.
Game da waɗanda aka ɗauka a dā a kan su wani abu ne, ko wane ne su, duk ɗaya ne a wurina; gama Allah ba ya nuna bambanci, ina dai gaya muku waɗannan da suke wani abu ne a dā, ba su ƙara mini kome ba.
Suka aiki almajiransu tare da mutanen Hiridus wurinsa. Suka ce, “Malam, mun san kai mutum ne mai mutunci, kuma kana koyar da maganar Allah bisa gaskiya. Mutane ba sa ɗaukan hankalinka, domin ba ka kula ko su wane ne ba.
Sai ’yan leƙen asirin suka tambaye shi, suka ce, “Malam, mun sani kana faɗin, kuma kana koyar da abin da yake daidai, ba ka kuma nuna bambanci, amma kana koyar da hanyar Allah bisa ga gaskiya.
Tun da yake kuna kira ga Uba wanda yake yin wa kowane mutum shari’a bisa ga ayyukansa ba bambanci, sai ku yi rayuwarku a nan kamar baƙi cikin tsoro mai bangirma.