aka kuma santa sosai saboda ayyuka masu kyau, kamar renon ’ya’ya, da karɓan baƙi, tana yi wa tsarkaka hidima, tana taimakon waɗanda suke cikin wahala tana kuma ba da kanta ga yin kowane aikin mai kyau.
Ku gai da Tiryifena da Tiryifosa, matan nan da suke aiki tuƙuru cikin Ubangiji. Ku gai da ƙaunatacciyata Fersis, wata matan da ta yi aiki tuƙuru cikin Ubangiji.
Ku gai da Anduronikus da Yuniyas, dangina waɗanda aka daure a kurkuku tare da ni. Su fitattu ne sosai a cikin manzanni, sun riga ni zama masu bin Kiristi.