Romawa 16:18 - Sabon Rai Don Kowa 202018 Gama irin waɗannan mutane ba sa bautar Ubangijinmu Kiristi, sai dai cikinsu. Ta wurin yaudara da kuma daɗin baki, suna ruɗin marasa wayo. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki18 Ai, irin waɗannan mutane ba sa bauta wa Ubangijinmu Almasihu, sai dai cikinsu. Ta romon kunne da daɗin baki suke yaudarar masu sauƙin kai. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Waɗannan mutane sun zama kamar ƙazanta a taronku na soyayya, suna ta ciye-ciye a cikinku, ba kunya ba tsoro. Su masu kiwo ne da suke ciyar da kansu kawai. Su kamar hadari ne da babu ruwa da iska take kori. Su kamar itatuwa ne, marasa ’ya’ya da rani, waɗanda aka tumɓuke, ko kamar itatuwan da aka tumɓuke suka kuma mutu ƙurmus.