Ka yi murna, kai matashi, a ƙuruciyarka, bari zuciyarka kuma tă yi farin ciki a kwanakin ƙuruciyarka. Ka bi shawarar zuciyarka da kuma duk abin da idanunka suka gani, amma ka sani fa, cikin dukan al’amuran nan Allah zai shari’anta ka.
Gama dole dukanmu mu bayyana a gaban kujerar shari’ar Kiristi, domin kowannenmu yă karɓi ladan aikin da ya yi a wannan jiki, ko mai kyau ne ko marar kyau.