A ƙarshe ’yan’uwa, sai wata rana. Ku yi ƙoƙari ku zama cikakku. Ku saurari roƙona, ku zama da tunani ɗaya, ku yi zaman salama. Allah na ƙauna da salama kuwa zai kasance tare da ku.
“Gishiri yana da daɗi, amma in ya rabu da ɗanɗanonsa, ta yaya za a sāke mai da ɗanɗanonsa? Ku kasance da gishiri a cikinku, ku kuma yi zauna lafiya da juna.”
Ka yi nesa da mugayen sha’awace-sha’awace na ƙuruciya, ka kuma bi adalci, bangaskiya, ƙauna da kuma salama, tare da waɗanda suke kira ga Ubangiji daga zuciya mai tsabta.