Na rubuta yadda na yi ne saboda sa’ad da na iso kada waɗanda ya kamata su faranta mini rai, su sa ni baƙin ciki. Na amince da ku duka a kan farin cikina naku ne ku duka.
Lokacin da abokan Ayuba su uku wato, Elifaz mutumin Teman, Bildad mutumin Shuwa, da Zofar mutumin Na’ama suka ji wahalar da ta auka wa Ayuba, sai suka shirya suka bar gidajensu suka je don su ta’azantar da shi.