35 “Wa ya taɓa ba wa Allah wani abu, da Allah zai sāka masa?”
35 “Wa kyauta ta shiga tsakaninsu da Allah, ya fara bayarwa, Har da za a sāka masa?”
Wane ne yake bi na bashi da dole in biya? Duk abin da yake ƙarƙashin sama nawa ne.
In kuna da adalci, me kuka ba shi, ko kuma me ya karɓa daga hannunku?
Wa ya ce ka fi sauran mutane? Me kuma kake da shi, wanda ba karɓa ka yi ba? In kuma karɓa ka yi, me ya sa kake taƙama kamar ba karɓa ba ne ka yi?
Ba ni da ikon yin abin da na ga dama da kuɗina ne? Ko kana kishi saboda ni mai kyauta ne?’