Ba na so ku kasance cikin rashin sani game da wannan asirin ’yan’uwa, domin kada ku ɗaga kai. Isra’ila sun ɗanɗana sashe na taurarewa har sai da shigowar Al’ummai masu yawa ya cika.
Kin dogara a muguntarki kika kuma ce, ‘Babu wanda ya gan ni.’ Hikimarki da saninki sun ɓad da ke sa’ad da kika ce wa kanki, ‘Ni ce, kuma babu wani in ban da ni.’
“Mutanena wawaye ne; ba su san ni ba. Su ’ya’ya ne marasa azanci; ba su da fahimi. Suna da dabarar aikata mugunta; ba su san yadda za su aikata alheri ba.”