60 Zuriyar ma’aikatan haikali da ta bayin Solomon su 392.
60 Jimillar zuriyar ma'aikatan Haikali da na Sulemanu, su ɗari uku da tasa'in da biyu ne.
Dukan zuriyar ma’aikatan haikali, da kuma bayin Solomon 392.
To, na farkon da aka sāke zaunar da su a mallakarsu a garuruwansu, su ne waɗansu Isra’ilawa, firistoci, Lawiyawa da kuma masu hidimar haikali.
Shefatiya, Hattil, Fokeret-Hazzebayim, da Amon.
Waɗansu sun hauro daga garuruwan Tel-Mela, Tel-Harsha, Kerub, Addon da Immer, amma ba su iya nuna cewa iyalansu su zuriyar Isra’ila ce ba,