Nehemiya 13:7 - Sabon Rai Don Kowa 20207 sai na koma zuwa Urushalima. A nan na ji game da mugun abin da Eliyashib ya aikata da ya tanada wa Tobiya ɗaki a filayen gidan Allah. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki7 Da na komo Urushalima, sai na ga mugun abin da Eliyashib ya yi domin Tobiya, yadda ya shirya masa ɗaki a filin Haikalin Allah. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Bayan an yi waɗannan abubuwa duka, sai shugabanni suka zo wurina suka ce, “Mutanen Isra’ila, har da firistoci da Lawiyawa ba su keɓe kansu daga maƙwabtansu ba, ba su kuma keɓe kansu daga irin rayuwar ƙazantar mutanen ƙasar ba, wato, rayuwar irinta Kan’aniyawa, da Hittiyawa, da Ferizziyawa, da Yebusiyawa, da Ammonawa, da Mowabawa, da Masarawa da Amoriyawa.