Nehemiya 13:5 - Sabon Rai Don Kowa 20205 ya kuma tanada masa babban ɗakin da dā ake ajiyar hadayun hatsi da turare da kayayyaki haikali, da kuma zakan hatsi, sabon ruwan inabi da kuma mai da aka umarta don Lawiyawa, mawaƙa da kuma matsaran ƙofofi, da kuma sadakoki domin firistoci. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki5 ya shirya wa Tobiya babban ɗaki inda dā aka ajiye hadaya ta gari, da turare, da tasoshi, da zakar hatsi, da ruwan inabi, da mai, waɗanda aka umarta a ba Lawiyawa, da mawaƙa, da masu tsaron ƙofofi, da inda aka ajiye sadakokin da ake ba firistoci. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
“Ban da haka ma, za mu kawo wa ɗakunan ajiyar gidan Allahnmu, abincinmu na farko daga ƙasa, na hadayun hatsinmu, na ’ya’yan dukan itatuwanmu da kuma na sabon ruwan inabinmu da mai namu wa firistoci. Za mu kuma kawo zakkar hatsinmu wa Lawiyawa, gama Lawiyawa ne ke karɓan Zakka cikin dukan garuruwan da muke noma.