Nehemiya 13:22 - Sabon Rai Don Kowa 202022 Sai na umarci Lawiyawa su tsarkake kansu su kuma tafi su yi tsaron ƙofofi don a kiyaye ranar Asabbaci da tsarki. Ka tuna da ni saboda wannan shi ma, ya Allahna, ka nuna mini jinƙai bisa ga madawwamiyar ƙaunarka. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki22 Sai kuma na umarci Lawiyawa su tsarkake kansu, su yi tsaron ƙofofin don a kiyaye ranar Asabar da tsarki. “Ya Allahna, ka tuna da wannan aiki nawa, ka rayar da ni saboda girman madawwamiyar ƙaunarka.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sai Yosiya ya umarci Hilkiya babban firist, tare da firistocin da suke taimakonsa, da masu tsaron ƙofa su kawar da dukan abubuwan da aka yi domin Ba’al, da domin Ashera, da kuma domin dukan rundunar taurari, daga haikalin Ubangiji. Ya ƙone su a bayan Urushalima a filayen Kwarin Kidron, ya kwashe tokan zuwa Betel.