Nehemiya 13:19 - Sabon Rai Don Kowa 202019 Sa’ad da inuwar yamma ya fāɗo a ƙofofin Urushalima kafin Asabbaci, na umarta a rufe ƙofofi kuma kada a buɗe sai Asabbaci ya wuce. Na kafa waɗansu mutanena a ƙofofin don kada a shigo da wani kaya a ranar Asabbaci. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki19 Magariba na yi kafin ranar Asabar, sai na yi umarni a rufe ƙofofin Urushalima, kada a buɗe su sai Asabar ta wuce. Na sa waɗansu barorina a ƙofofin, don kada su bari a shigo da kaya ran Asabar. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Na ce musu, “Kada a buɗe ƙofofin Urushalima da sassafe sai rana ta fito sosai. Yayinda matsaran ƙofofi suna aiki, a kulle ƙofofin a sa musu sakata kafin matsaran su tashi, wajen fāɗuwar rana. Ku kuma naɗa mazaunan Urushalima a matsayin masu tsaro, waɗansunsu a wuraren aiki, waɗansun kuma kusa da gidajensu.”