Nehemiya 13:15 - Sabon Rai Don Kowa 202015 A waɗannan kwanaki, na ga mutane a Yahuda suna matse ruwan inabi a ranar Asabbaci suna kuma kawo hatsi suna labta su a kan jakuna, tare da ruwan inabi, ’ya’yan inabi, ɓaure da kaya iri-iri. Suna kuma kawowa dukan wannan cikin Urushalima a ranar Asabbaci. Saboda haka na gargaɗe su a kan sayar da abinci a wannan rana. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki15 A kwanakin nan na ga mutane a Yahuza suna matse ruwan inabi, suna labta wa jakunansu buhunan hatsi, da ruwan inabi, da 'ya'yan inabi, da ɓaure, da kaya iri iri, suna kawo su cikin Urushalima a ran Asabar. Sai na yi musu faɗa a kan sayar da abinci a wannan rana. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |