Nehemiya 10:29 - Sabon Rai Don Kowa 202029 dukan waɗannan yanzu suka sadu da manyan gari ’yan’uwansu, suka rantse, cewa la’ana ta same su idan ba su kiyaye Dokar Allah da aka bayar ta wurin Musa bawan Allah su kuma mai da hankali ga yin biyayya da dukan umarnai, ƙa’idodi da farillan Ubangiji shugabanmu ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki29 suka haɗa kai da 'yan'uwansu, da shugabanninsu, suka rantse, cewa la'ana ta same su idan ba su kiyaye dokokin Allah waɗanda ya ba bawansa Musa ba. Suka rantse za su kiyaye, su aikata umarnai, da ka'idodi, da dokokin Ubangijinmu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sarki ya tsaya dab da ginshiƙi ya kuma sabunta alkawarin a gaban Ubangiji, ya ce zai bi Ubangiji, yă kiyaye dokokinsa, da ƙa’idodinsa, da farillansa, da dukan zuciyarsa da dukan ransa, ta haka ya tabbatar da kalmomin alkawarin da yake a rubuce a cikin littafin nan. Sa’an nan dukan mutane ma suka yi alkawari yin haka.
“Yanzu fa Ubangiji, Allah na Isra’ila, ka kiyaye wa bawanka Dawuda mahaifina alkawuran da ka yi masa sa’ad da ka ce, ‘Ba za ka kāsa kasance da mutumin da zai zauna a gabana a kan kujerar sarautar Isra’ila ba, in kawai ’ya’yanka maza za su kula cikin dukan abin da suke yi su yi tafiya a gabana bisa ga dokata, kamar yadda ka yi.’