Za mu sāke ƙin yin biyayya da umarninka mu yi auratayya da mutanen nan da suke aikata waɗannan abubuwan banƙyama? Ba za ka yi fushi da mu, ka ƙone mu da fushinka har babu ɗan saura ba?
“ ‘Duk da haka mutanen Isra’ila suka yi mini tawaye a cikin hamada. Ba su bi ƙa’idodina ba amma suka ki dokokina, ko da yake mutumin da ya yi biyayya da su zai rayu ta wurinsu, suka ɓata Asabbataina ƙwarai. Saboda haka na ce zan zuba hasalata a kansu in kuma hallaka su a hamada.