M.Sh 7:13 - Sabon Rai Don Kowa 202013 Zai ƙaunace ku, yă albarkace ku, yă kuma ƙara yawanku. Zai albarkaci ’ya’yanku, amfanin gonarku; hatsinku, sabon ruwan inabinku da kuma mai, ƙanana shanunku, da ’yan tumaki na tumakinku, a ƙasar da ya rantse wa kakanninku cewa zai ba ku. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki13 Ubangiji zai ƙaunace ku, ya sa muku albarka, ya riɓaɓɓanya ku. Zai sa wa 'ya'yanku albarka, ya yalwata amfanin gonarku, da hatsinku, da inabinku, da manku, da garken shanunku, da 'yan ƙananan garkenku a ƙasar da ya rantse wa kakanninku zai ba ku. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
“To yanzu, ya Allahnmu, mai girma, mai iko, da kuma mai banrazana, wanda yake kiyaye alkawarinsa na ƙauna, kada ka bar dukan wannan wahala ta zama kamar marar muhimmanci a idanunka, wahalar da ta zo a kanmu, a kan sarakunanmu da shugabanni, a kan firistocinmu da annabawa, a kan kakanninmu da kuma dukan mutanenka, daga kwanakin sarakunan Assuriya har yă zuwa yau.