M.Sh 6:21 - Sabon Rai Don Kowa 202021 Sai ku gaya musu, “Dā mu bayin Fir’auna ne a Masar, amma Ubangiji ya fitar da mu daga Masar da hannu masu ƙarfi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki21 sai ku amsa wa 'ya'yanku, ku ce, ‘Dā mu bayin Fir'auna ne a ƙasar Masar, amma Ubangiji ya fisshe mu daga Masar da dantse mai iko. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Akwai wani allahn da ya taɓa yin ƙoƙari yă ɗauko wa kansa wata al’umma daga wata al’umma, ta wurin gwaje-gwaje, ta wurin alamu masu banmamaki da al’ajabai, ta wurin yaƙi, ta wurin hannu mai iko, da kuma hannu mai ƙarfi, ko kuwa ta wurin ayyuka masu bangirma da na banmamaki, kamar dukan abubuwan da Ubangiji Allahnku ya yi saboda ku a Masar, a kan idanunku?