7 “Ba za ka kasance da waɗansu alloli a gabana ba.
7 “ ‘Kada ka kasance da waɗansu gumaka, sai ni.
“Ba za ka yi wa kanka waɗansu alloli ba sai ni.
Sai Yesu ya ce masa, “Rabu da ni, Shaiɗan! Gama a rubuce yake, ‘Yi wa Ubangiji Allahnka sujada, shi kaɗai kuma za ka bauta wa.’”
’Ya’yana ƙaunatattu, ku yi nesa da gumaka.
don kowa yă girmama Ɗan kamar yadda yake girmama Uban. Wanda ba ya girmama Ɗan ba ya girmama Uban, da ya aiko shi ke nan.
Kada ku kasance da baƙon allah a cikinku; ba za ku rusuna ga baƙon allah ba.
Kada ku bi waɗansu alloli, allolin mutanen da suke kewaye da ku;
Ku yi hankali, kada a ruɗe ku har ku bauta wa alloli, ku kuma yi musu sujada,
Ni ne Ubangiji Allahnku wanda ya fitar da ku daga Masar. Ku buɗe bakinku zan kuwa cika shi.