M.Sh 5:14 - Sabon Rai Don Kowa 202014 amma rana ta bakwai, Asabbaci ne ga Ubangiji Allahnka. A kanta ba za ka yi wani aiki ba, ko kai, ko ɗanka, ko ’yarka, ko bawanka, ko baiwarka, ko saniyarka, ko jakinka, ko wani daga dabbobinka, ko baƙo a ƙofofinka, don bayinka maza da mata su ma su huta, kamar ka. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki14 Amma rana ta bakwai ranar hutu ce ta Ubangiji Allahnka. A cikinta ba za ka yi kowane irin aiki ba, kai da ɗanka, da baranka, da baranyarka, da sanka, da jakinka, da kowace dabbar da kake da ita, da baƙon da yake zaune tare da kai, don barorinka mata da maza su ma su huta kamarka. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
A waɗannan kwanaki, na ga mutane a Yahuda suna matse ruwan inabi a ranar Asabbaci suna kuma kawo hatsi suna labta su a kan jakuna, tare da ruwan inabi, ’ya’yan inabi, ɓaure da kaya iri-iri. Suna kuma kawowa dukan wannan cikin Urushalima a ranar Asabbaci. Saboda haka na gargaɗe su a kan sayar da abinci a wannan rana.