M.Sh 33:29 - Sabon Rai Don Kowa 202029 Kai mai albarka ne, ya Isra’ila! Wane ne yake kamar ka, mutanen da Ubangiji ya ceta? Shi ne mafakarka da mai taimakonka da kuma takobinka mai ɗaukaka. Abokan gābanka za su zo neman jinƙai a gabanka, za ka kuwa tattake masujadansu.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki29 Mai farin ciki ne kai, ya Isra'ila! Wane ne kamarku, mutanen da Ubangiji ya ceta? Ubangiji ne garkuwarku, Shi ne kuma takobinku mai daraja. Magabtanku za su yi muku fādanci, Amma ku za ku tattake masujadansu.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Akwai wani allahn da ya taɓa yin ƙoƙari yă ɗauko wa kansa wata al’umma daga wata al’umma, ta wurin gwaje-gwaje, ta wurin alamu masu banmamaki da al’ajabai, ta wurin yaƙi, ta wurin hannu mai iko, da kuma hannu mai ƙarfi, ko kuwa ta wurin ayyuka masu bangirma da na banmamaki, kamar dukan abubuwan da Ubangiji Allahnku ya yi saboda ku a Masar, a kan idanunku?