M.Sh 32:21 - Sabon Rai Don Kowa 202021 Sun sa ni kishi ta wurin abin da ba allah ba, suka kuma husata ni da gumakansu na wofi. Zan sa su yi kishi ta wurin waɗanda ba mutane ba; zan sa su yi fushi ta wurin al’ummar da ba ta da sani. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki21 Suka sa ni kishi da abin da ba Allah ba, Suka tsokani fushina da gumakansu, Ni kuma zan sa su su yi kishi da waɗanda suke ba mutane ba. Zan tsokane su da wawanyar al'umma. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Suka yi watsi da farillansa da yarjejjeniyar da ya ƙulla da kakanninsu, da kuma kashedin da ya yi musu. Suka bi gumaka marasa amfani, wannan ya sa su ma kansu suka zama marasa amfani. Suka kwaikwayi sauran ƙasashen da suke kewaye da su, ko da yake Ubangiji ya umarce su cewa, “Kada ku yi rayuwa irin tasu,” suka kuwa yi abin da Ubangiji ya hana su.