M.Sh 32:15 - Sabon Rai Don Kowa 202015 Yeshurun ya yi ƙiba, ya yi kauri; cike da abinci, ya zama da nauyi, ya kuma zama sumul. Ya yashe Allahn da ya yi shi, ya ƙi Dutse Cetonsa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki15 “Yeshurun ya yi ƙiba, yana harbin iska, Ka yi ƙiba, ka yi kauri, ka yi sumul. Ya rabu da Allahn da ya yi shi, Ya raina Dutsen Cetonsa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Suka kame birane masu katanga masu ƙarfi, da ƙasa masu ba da amfani; suka mallaki gidaje cike da kowane irin abu mai kyau, da rijiyoyin da aka riga aka haƙa, da gonakin inabi, da gonakin itatuwan zaitun da kuma itatuwan ba da ’ya’ya a yalwace a ciki. Suka ci suka ƙoshi, suka kuma yi ƙiba; suka ji daɗi cikin alherinka mai girma.