M.Sh 32:14 - Sabon Rai Don Kowa 202014 da kindirmo da madara daga shanu da tumaki da ƙibabbun tumaki da awaki, da zaɓaɓɓun ragunan Bashan da kuma ƙwayoyin alkama mafi kyau. Ka sha ruwan inabi ja wur mai kumfa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki14 Ya sami kindirmo daga shanu, Da madara daga garken tumaki da na awaki, Da kitse daga 'yan raguna, da raguna, Da bijimai, da bunsurai daga Bashan, Da alkama mafi kyau. Ka sha ruwan inabi jaja wur, mai kyau. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Suka kame birane masu katanga masu ƙarfi, da ƙasa masu ba da amfani; suka mallaki gidaje cike da kowane irin abu mai kyau, da rijiyoyin da aka riga aka haƙa, da gonakin inabi, da gonakin itatuwan zaitun da kuma itatuwan ba da ’ya’ya a yalwace a ciki. Suka ci suka ƙoshi, suka kuma yi ƙiba; suka ji daɗi cikin alherinka mai girma.