Yau, na kira sama da duniya, su zama shaidata a kanku. Idan kuka yi rashin biyayya, lalle za ku hallaka nan da nan daga ƙasar da kuke ƙetare Urdun ku gāda. Ba za ku daɗe a cikinta ba, amma za a kawar da ku ƙaƙaf.
Ku tattara dukan dattawan kabilanku, da kuma dukan hafsoshinku a gabana, saboda in faɗa waɗannan kalmomi a kunnuwansu, in kuma kira ga sama da ƙasa su zama shaida a kansu.
A wannan rana na kira bisa sama da ƙasa a matsayin shaidu a kanku, cewa na sa a gabanku rai da mutuwa, albarku da la’anoni. Yanzu sai ku zaɓi rai, saboda ku da ’ya’yanku ku rayu
Ku zo kusa, ku al’ummai, ku kuwa saurara ku kasa kunne, ku mutane! Bari duniya ta ji, da kuma dukan abin da yake cikinta, duniya, da dukan abin da yake fitowa daga gare ta!